Daya daga cikin manyan batutuwan da suka
kankane kafofin yada labaran mu cikin makwannin da suka gabata shi ne batun
neman yi wa tsarin mulkin Nigeria kwaskwarima ta yadda zai ba jihohi damar
kirkiro rundunonin ‘yansanda na kashin kan su.
An samu ra’ayoyi mabambamta daga muhawawar da ake ci gaba da tafkawa akan
dacewa ko rashin dacewar wannan mataki. Alal misali, masu muradin ganin
tabbatar wannan manufa ta kirkiro ‘yansandan jihohi na nuni da cewa hakan zai
ba Gwamnonin jihohi damar karfafa matakan tsaro da kuma shawo kan rikice-rikice
a jihohin nasu cikin hanzari ba tare da dogaro da Gwamnatin tarayya ba. Su kuma wadanda suka saba wa wannan ra’ayi cewa
suke yi yin hakan ba zai haifa wa kasar nan da mai ido ba musamman idan akayi
la’akari da cewa abu ne mai sauki wadannan ‘yansanda su zama ‘yan bangar siyasa
ga Gwamnatocin da suka kafa su wanda hakan zai basu damar tursasawa abokan
adawar siyasa.
Bayan yin la’akari da wadannan ra’ayoyi
mabambamta tunani na yafi karkata akan cewa rashin alfanun dake tattare da
wannan shiri ya nunka alfanun dake tattare da shi. Misali, sanin kowa ne cewa rashin adalcin
tsarin siyasar mu yasa cin zabe a kasar nan ya ta’allaka ne kacokan akan zurfin
aljihun mai neman mukami maimakon kyakyawar manufa ta ci gaban kasa da yalwatar
arziki; wato irin shugabancin da ya kamata ya taimaka wajen rage matsanancin
talauci dake addabar kasa da jama’arta, samar da ayyukan yi da kuma rage
wagegen gibin da dake tsakanin masu shi da marasa shi. A sakamakon haka sai ya
kasance ‘yan siyasar mu suna kwadayin kama madafun iko ko ta halin kaka har ta
hanyar gwara kawunan talakawa da janyo hasarar dukoyoyi da rayukan bil’adama.
Wannan shi ya jaza musu daukar nauyin ‘yan gani-kashenin-siyasa wadanda basu
dauki ran bil’adama a bakin komai ba.
A kudancin kasar nan inda wannan kira na
kafa ‘yansandan jihohi yafi samun gindin zama sanin kowa ne cewa suna da irin
wadannan ‘yan bangar siyasa kamar kungiyoyi irin na OPC, da Egbesu Boys, da Bakasi
Boys, da ‘yan a fasa-kowa-ya-rasa na kungiyar nan mai hakilon farfado da yunkurin
tabbatar da kafuwar kasar Biafra wato MASSOB da kuma dimbin kungiyoyin ‘yan
tsagerar yankin Neja-Delta masu tafka ta’addanci da sunan bibiyar hakkokin
jihohi masu albarkatun man fetur. Anan jihohin mu na Arewa ma ‘yan siyasar mu
na da nasu ‘yan banga da ke amsa sunaye dabam-dabam.
Bisa la’akari da wannan babu tantama
akan cewa kirkiro ‘yansandan jihohi zai zama wata hanya ta halatta wadannan baragurbin
kungiyoyi don kare muradun siyarsar wasu ‘yan tsirarun Jama’a. Kuma wannan
tabbas zai haifar da tashin-tashina a cikin al’umma musamman idan aka yi
la’akari da cewa galibin wadanda Gwamnatocin nan zasu dauka a matsayin ‘yan
sandan jiha ‘yan barandar siyasar su ne.
Bayan haka bincike ya nuna cewa kusan kashi
saba’in cikin dari na rigingimu tsakanin al’umma a caji ofis ake kashe su
kimanin kashi talatin cikin dari ne ke dangana wa da kotu. To idan haka ne me
kake tsammanin zai faru idan rashin jituwa ta shiga tsakanin Bahaushe mazaunin
Legas and Bayarabe dan kasa kuma maganar ta kai caji ofis inda kusan duk Jami’an
‘yan sandan da za su yi hukunci kan batun ‘yan kabilar yarbawa ne; ko kuma a
Sabon Garin Kano irin wannan rikici ya wakana tsakanin dan kabilar Ibo da Bahaushe
dan gari? A irin wannan hali zai yi matukar
wuya a samu tabbatar da adalci ko kuma in ma an yi adalcin abokin shara’a ya
yarda cewa lallai an yi adalci ba tare da nuna kabilanci ko bangaranci ba. Kada
mu manta cewa wannan kasa ce mai cike bambamce-bambamcen addini, harshe, da
asali wadanda abubuwa ne masu tasirin gaske cikin zamantakewar jama’a da yadda
suke kallon al’amuran rayuwa.
Kuma ya kamata mu duba mu gani shin Gwamnatocin
jihohin nan da ake magana akai suna da karfin tattalin arzikin da su iya daukar
nauyin ‘yansanda na kashin kansu kuwa? Kada mu manta cewa kwanan aka yi ta
dauki-ba-dadi tsakanin gwamanonin jihohi da ‘yan kungiyar kwadago akan batun
mafi karancin albashi na Naira dubu goma sha takwas. Galibin jihohin kasar nan sun ta koka wa kan rashin
karfin biyan wannan tsarin albashi har ta kai wasun su ga yin barazanar rage
yawan ma’aikata in har aka dage kan cewa sai sun biya. To yaushe wanda ke kukan
targade zai nemi karaya kuma! Sanin kowa
ne cewa ayau akwai Gwamnatocin jihohin dake shafe watanni biyar zuwa shida ba
tare da sun biya albashi ba. Me kake gani zai faru idan ka kwashe irin wannan
tsawon lokaci baka biya mutumin dake da bindiga da doka a hannun sa ba? Tabbas
wannan zai kara tsananta matsalar cin hanci da rashawa da karuwar manyan
laifuka kamar su fashi da makami da ci-da-ceto a tsakanin al’umma.
Bugu da kari kirkiro ‘yansandan jihohi
saboda sinadarin siyasar dake cikinsa zai kawo yawan korar horarrun ma’aikata a
bisa dalilan siyasa. Wannan zai kasance haka ne saboda duk gwamanatin da ta hau
karagar mulki burin ta shi ne ta samu Jami’an ‘yansandan da zasu taimaka mata
wajen kare muradun ta na siyasa ko da kuwa yin hakan zai jaza sallamar
ma’aikatan da ake ganin suna da alaka da siyasun adawa ne. Idan aka fara yi wa sha’anin tsaro irin
wannan rikon-sakainar-kashi tabbas al’umma zata shiga cikin rudani wanda ba zai
misaltu ba.
Saboda dalilan da na ambata a sama da ma
wadansu wadanda karancin wuri da lokaci ba zai bada damar a yalwata bayani akan
su ba, ya zama wajibi ayi watsi da wannan gurguwar shawara ta neman a kirkiro
‘yan sandan jihohi. Maimakon haka kamata
yayi mu duba muga yadda zamu karfafa rundunar ‘yansanda ta kasa da muke da ita
a yanzu don karkata akalar ta wajen yi wa kasa aiki cikin gaskiya, da adalci,
da sanin mutuncin kai da kishin kasa.
Daya daga cikin hanyoyin da za’a iya bi
wajen tabbatar da wannan muradi shi ne ta hanyar cire akidar nan ta cin hanci
da rashawa a tsakanin jami’an tsaron mu.
Samun hakan ya tabbata kuwa sai an koma ga tushe wato tun daga lokacin
da za’a dauki dan sanda aiki. Dole ne ya
zama wadanda za’a dauka aikin dan sanda sune wadanda suka fi cancanta ta fuskar
ilimi, kirar jiki, koshin lafiya, gaskiya, rikon amana da sanin ya kamata. Sabanin haka ayau rahotanni da dama na nuni da
yadda ake karbar makudan kudade a hannun matasa don shigar da su wannan
aiki. To a gaskiya wannan shi ne matakin
farko na cusa akidar cin hanci da rashawa a tsakanin ‘yansandan mu. Don kuwa kowa ya shiga aiki ta irin wannan
hanya kokarin sa a koda yaushe shi ne ya zai mayar da kudinsa ya nunka maimakon
ciyar da kasa gaba ta hanyar kare rayuka da mutuncin al’umma da dokokin aiki.
Bayan haka, zai yi kyau idan aka
kyautata hanyar sadarwa tsakanin shugaban kasa da gwamnoni musamman akan
al’amuran tsaro ta yadda zai zama su (Gwamnoni) suna da hanyoyin tuntuba na kai
tsaye tsakanin su da shugaban kasa da shugaban ‘yansanda. Hakan zai bada damar
dauka da kuma wanzar da matakan tsaro cikin hanzari a duk lokacin da bukatar
yin hakan ta taso. Kuma wajibi ne
hukumomi su ci gaba da kiyaye hakkokin ‘yansanda ta hanyar biyan su wadataccen
albashi kuma a kan kari. Bugu da kari ya
wajaba a samar wa ‘yan sanda wadatattu kuma ingantantattun kayan aiki na zamani. Abin da matukar ban takaici ace a yau ‘yan
ta’adda da masu aikata muggan laifuka suna da makaman da amon su kawai ya isa
ya firgita Jami’an tsaron mu.
Haka zalika ya kamata aba ‘yansandan mu
cikakken horo akan yaki da manyan laifuka ta hanyar leken asiri domin hakan ne
zai basu damar bankadowa da dakile duk wani shiri na aikata laifi tun kafin
akai ga aikata shi. Cin nasarar wannan
buri zai samu ne ta hanyar samar da kayan aikin yaki da manyan laifuka na
zamani irin su na’ura mai kwakwalwa, da girke kyamarori masu nadar hotuna da
bayanai a wuraren hada-hadar Jama’a.
Saboda haka dole Gwamnati tayi kasafi na musamman don samar da wadannan
na’urori da kuma ba Jami’an tsaron mu ingantaccen horon da zai basu damar
sarrafa su don amfanin kasa. A wannan
gaba kuma wajibi ne sassan tsara dabarun tsaron kasa na hukumar ‘yansanda su yi
la’akari da karfafa dabarar yada ‘yansandan ciki a tsakanin al’umma. Wannan zai
taimaka gaya wajen gano bata-gari a da kuma yin maganin su tun kafin su kai ga
yiwa Jama’a illa.
A karshe, wajibi ne a ba ‘yansandan mu
horo na musamman akan dabarun hulda da Jama’a. Ya zama dole ‘yansanda su
siffanta da wannan kirari na su na “Dan Sanda Abokin Kowa”. Halin da muke ciki
yanzu inda galibin al’umma ke yi wa ‘yansanda kallon azzalumai masu neman
hanyoyin kuntata wa Jama’a dole ne ya canza.
Babbar hanyar canza irin wannan tunani shi ne ta hanyar kyautata huldar
Jami’an tsaro da al’umma da shugabannin su.
Anan ya zama wajibi sashen hulda da Jama’a na hukumar ya samar da wani
tsari na tuntubar juna tsakanin ‘yansanda da dattawan gari, shugabannin addini,
shugabannin kungiyoyin matasa da na mata da na dalibai da dai sauransu. Wannan shi zai bada damar hada karfi da karfe
don yakar muggan laifuka a cikin al’umma. Dama ai ance hannu daya baya daukar
jinka!